Kotu mafi girma ta Majalisar Dinkin Duniya ta umurci kasar Senegal, cewa au ta tuhumi tsohon Shugaban Chadi Hissene Habre da aikata kisan kiyashi, au ta tasa keyarsa zuwa kasarsa ba tare da bata lokaci.
Kotun Kasa da Kasar da ke birnin Hague ta yanke shawarar ce jiya Jumma’a, bayan da kasar Belgium ta gabatar da bukatar gurfanar da Mr. Habre a kotu, bisa zargin cin zarafin bil’adama.
Wani Kwamitin Sasantawa ta kasar Chadi, ya ce Habre ne ke da alhakin kuntatawar da aka yi saboda dalilai na siyasa, da kuma kashe-kashen mutane akalla 40,000. Kwamitin ya ce wannan cin zarafin da ake zargin an yi, ya faru ne cikin tsawon shekaru 8 da ya yi mulki, wanda ya fara daga 1982.
Habre ya cigaba da zama a Senegal tun bayan da Shugaba mai ci, Idris Deby ya hambarar da shi.