Da take gabatar da hukuncin, kotun mai Alkalai biyar da mai shari’a Jummai Hanatu Sankey ke shugabanci ta ce kotun ta yi watsi da tsigewar, kan hujjar keta hakkin tsohon gwamna Nyako na rashin ba shi damar kare kansa daga tuhumar da majalisar ke masa.
Kuma bisa ka’ida inji kotun kotun tilas ne ta mika masa takardar tuhumar hanu-da-hanu. Sharadin da majalisar ta kasa cikawa.
Sai dai sugunne bata kare ba inji kwamishina shara’a na jihar Adamawa, Barr. Silas Bala Sanga saboda majalisar dokokin jiha zasu daukaka kara zuwa kotun koli.
Ko da yake hukuncin da kotun ta yanke, ya maida wa tsohon gwamna Murtala Nyako martabarsa, sai dai ba zai koma kan karagarsa ba saboda karewar wa’adinsa tun daga ranar 29 ga watan Mayun 2015, idan za a iya tunawa majalisar dokokin jihar Adamawa ta tsige tsohon gwamnan ne ranar 16 ga wata Yulin 2015, da kuri’u 17 cikin 25, bisa samunsa da laifin zarge zarge 15 da ake tuhumarsa da su.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5