Tsoffin Shugabannin Amurka Sun Hadu A Taron Agaji

  • Ibrahim Garba

Shugabannin Amurka da su ka gabata: Jimmy Carter, da George W. Bush da George H. W. Bush da Bill Clinton da Kuma Barack Obama

Tsoffin Shugabannin Amurka biyar da ke raye, sun yi amfani da tasirinsu wajen janyo dinbin masu bayar da gudunmawa ga wadanda bala'o'in mahaukaciyar guguwa su ka rutsa da su a ciki da kewayen Amurka.

Dukkannin Shugabannin Amurka na da da ke raye su biyar, sun halarci wani bikin kade-kade jiya Asabar na tara gudunmowa ma wadanda mahaukaciyar guguwa ta rutsa da su, a wasu jahohin Amurka da yankunan kasar Puerto Rico da Virgin Islands, wadanda su ma mallakin Amurka ne.

Shugabannin na da, Barack Obama da George W Bush, da Bill Clinton da George H.W. Bush da Jimmy Carter sun halarci shagalin kade-kaden, wanda aka yi a College Station, jahar Texas jiya Asabar.

Shugaba Donald Trump bai hallara ba, to amma an nuna shi ta kafar video ya na gode ma Shugabannin na da da kuma sauran mutanen da su ka bayar da gudunmowa.