Dukkan tsoffin shugabannin Amurka dake raye sun halarci wani gangamin kade kade da raye raye da aka shirya domin tara kudi don tallafawa wadanda bala'in mahaukatan guguwar iska da ruwan sama suka yiwa barna anan Amurka da kuma wasu yankunanta na Puerto Rico da tsibiran Virgin.
Tsoffin shugabanni Barack Obama, George Bush babba da karami,Jimmy Carter Bill Clinton sun halarci gangamin a filin wasanni na jami'ar Txas A&M.
A wani mataki na nuna hadin ba kasafai ba, shugaban Amurka Donald Trump wanda bai halarci gangamin kai tsaye ba, ya tura sako ta vidiyo, inda ya godewa tsoffin shugavbannin saboda muhimmiyar rayawa da suka tada "saboda taimkawa 'yan uwanmu Amurkawa su farfado."
Dukkan tsoffin shugabannin sun yi magana inda suka yaba da kokarin Amurkawa na ganin sun tallafawa 'yan uwansu 'yan kasar wadanda wannan bala'i ya afkawa.