NIAMEY, NIGER - Biyo bayan kiran da hukumomin Jamhuriyar Nijar suka wa rundunar kar ta kwana, da ta hada da tsohin soja da ‘yan sanda da suka yi ritaya, haka ma da jendarma da gardi, da tsoffin kwastam da sojojin daji da ma jami'an tsaron da suka nemi su ajiye aiki bayan shekaru 5 suna tsaron kasa da ma sauran su, wadansu daga cikin tsofin askarawan sun ce amsa kira.
Tsoffin jami'an tsaron sun ce a shirye suke da su sake komawa fagen daga domin kare wannan kasar da ‘yan ta'adda suka zagaye ta daga gabas a tafkin bakin Chadi da yammacin kasar a iyaka da Mali da Burkina Faso a arewa da Algeriya da Libya yayin da 'yan bindiga dadi ke kutsowa daga Najeriya.
Abdurahamane Idrissa Kado Soja daya ne daga cikin su, wadansu tsoffin sojan na gamu da su a Birni N'Konni, sun ce shirye suke, su sake yin damara domin komawa fagen daga don a yi ta ta kare.
Wannan kiran da hukumomin kasar suka yi wa rundunar kar-ta-kwana zai kara karfafawa askarawan kasar da adadinsu ya haura dubu talatin a halin yanzu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Harouna Mamane Bako:
Your browser doesn’t support HTML5