Tsaurara Sharuddan Zama Ba’amurke: ‘Yan Democrats Sun Ruga Kotu

Shugaba Donald Trump

Kamar yadda aka zaci zai faru, bayan da Shugaba Donald Trump ya yi amfani da ikonsa na shugaban kasa ya tsaurara sharuddan zama dan kasa, 'yan jam'iyyar Democrats sun ce ba za ta sabu ba.

Jihohin Amurka 22 karkashin jam'iyyar Democrat’s sun shigar da kara a jiya Talata akan umarnin zartarwa da shugaba Donald Trump ya sanya wa hannu na kawo karshen bada shaidar zama dan kasa ta haihuwa ga 'ya'yan bakin haure da ke zaune a Amurka.

Gwamnatocin birnin Washington, D.C. da San Francisco na daga cikin sahun farko a Jihohin da su ka shigar Kararrakin, wadanda ke adawa da umarnin zartarwa na Trump din, wanda ya sanyawa hannu sa'o'i kadan bayan rantsar da shi a ranar Litinin.

Kundin tsarin mulkin Amurka ya ba da tabbacin zama dan kasa ga wadanda aka haifa a kasar.

Ammam Trump ya sanya hannu akan umarnin zartarwar, a wani bangare na rage yawan bakin haure miliyan 11 ko fiye da ke zaune a Amurka, dokar da ta umurci hukumomin Amurka da su daina baiwa bakin haure takardar zama dan kasa idan sun haihu.

Umarnin shugaban na Republican ya umurci jami'an gwamnatin tarayya cewa daga ranar 19 ga watan Fabrairu, da su daina bada shaidar zama dan kasar Amurka ga yaran da aka haifa a Amurka.