Gamayyar kungiyoyin arewacin kasar tare da wasu kungiyoyin mata masu fafutukar kare hakkin dan’adam sun bayyana cewa lokaci yayi da kowa yakamata ya fito ya kare kansa sabida abin da suka kira da cewa gwamnati ta gaza wajen samar da tsaro ga al’ummarta
A cikin sati biyun da suka gabata jihohin Sokoto da Zamfara, Kaduna da katsina har da Jihar Neja sun fuskanci matsalar hare hare da aka kwatanta da mafi muni da kuma tashin hankali inda aka kashe mata har da kananan yara, lamarin da ya sa gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya karkashin jagorancin Nastura Ashir Sherif su ka suka bukaci hada taron masu ruwa da tsaki daga yankin don kare kawunansu.
Su ko wasu kungiyoyin matan arewa masu fafutukar kare hakkin dan’adam gangamin zaman dirshen suka fara a filin dandalin Unity Fountain dake Abuja a ranar Juma’a, inda suka ce ba za su bari ba har sai gwamnati ta nemo bakin zaren matsalar. Za kuma su cigaba da zaman dirshe.
Kan batun gazawar gwamnati wajen daukar matakan da suka kamata Kwararre kan sha’anin tsaro a Najeriyar Yahuza Ahmed getso ya yi kira da cewa shugaba Buhari ya bada umarnin cewa duk wanda a gani da makamai da bai kamata ba, to lallai a dauki mataki a kanshi, idan gwamnati za ta tashi tsaye, kamata yayi a dauki ma'aikata kuma a horar da su, a tauna tsakuwa, domin aya ta ji tsoro.
A halin da ake ciki 'yan Najeriya da dama na da ra’ayin daukar matakin zare kansu idan har gwamnati ta cigaba da gazawa wajen kare al’ummarta.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim:
Your browser doesn’t support HTML5