Tun gabanin nan hukumomi a kasar Jodan sun tabbatar da mutuwar alhazan su tsoffi 14 yayin da 17 su ka bace a Jabal Rahama a Arfa.
Babban likitan alhazan Najeriya Dr.Abubakar Adamu Isma’ila ya tabbatar da mutuwar wata 'yar Najeriya daya a sanadiyyar zafin. Ya kuma bayyana matakan da suke dauka domin fadakar da tawagar kan illar zafin ranar. “mun yi iya kokarin fadakarwa kan illar zafin rana don samawa maniyyata sa’ida amma kaddara ta auku. Mu na kara kiran alhazai su dauki matakin yawaita shan ruwa.”
A hirar ta da Muryar Amurka, jami’ar watsa labaru ta hukumar alhazan Najeriya Fatima Sanda Usara ta bayyana yadda su ka yi ta kokarin agazawa alhazai da zafin ranar ya galabaitar.
Da ya ke zagawa rumfunan alhazai, gwamnan Katsina Dikko Radda ya bayyana rasuwar wani alhaji daga jihar Katsina wanda ya rasu yayin zaman arfa.
An yi harsashen cewa, wadanda su ka mutu na iya fin wadannan da a ka ji a yanzu. Bisa ga tsarin Najeriya, za a ji cikakkun alkaluman a taron da hukumar kan yi bayan kammala dukkan ayyukan hajji.
Sama da mahajjata 2,760 ne suka yi fama da zazzabin da matsanancin zafin rana ke haifarwa ranar Lahadi kadai a farkon zagayen farko na jifan shaidan, a cewar ma’aikatar lafiyar kasar Saudiya.
Fiye da Musulmai miliyan 1.83 ne suka yi aikin Hajji bana, kasa da miliyan 1.84 da su ka je aikin hajji bara, kamar yadda ma’aikatar kula da aikin hajji da Umra ta Saudiyya ta fitar. Alkaluman na bana sun hada da mahajjata sama da miliyan 1.6 daga kasashe 22, da kuma ‘yan kasar Saudiyya da mazauna kusan 222,000.
Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar:
Your browser doesn’t support HTML5