Tsadar Rayuwa Na Hana Mutane Zuwa Asibiti-Likitoci

Ziyarar CNDH Zuwa Asibiti

Kwararru a fannin lafiya sun koka cewa, marasa lafiya da dama basu zuwa asibiti sai cutar da su ke fama da ita ta ta’azzara sabili da matsanancin kuncin rayuwa.

Binciken da Muryar Amurka ta gudanar na nuni da cewa, duk da sanin hadarin da ke tattare da rashin zuwa asibiti kan lokaci, mutane da dama a Najeriya sun gwammace jinyar kansu a gida sabili da rashin kudin jinya, abinda kwararu su ka bayyana a matsayin wani lamari mai hatsarin gaske da ke sanadin rasa rayukan mutane da dama.

A wani lokaci baya, Ministan lafiya Dokta Muhammad Ali Pate ya nuna damuwa kan yadda tsadar kayan jinya kan kawo cikas wajen kula da bukatun kiwon lafiya a Najeriya, inda ya nuna bukatar samar da wasu kayan da su ka hada da magunguna daga cikin gida.

Hatta tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana illar da ya samu a sanadiyyar yi wa kai magani ba tare da zuwa asibiti ba wanda ya sa ya shawarci mutane su gujewa hakan.

Kwanannan gwamnatin Najeriya ta sanar da yiwa mata masu juna biyu da basu da galihu tiyatar haihuwa kyauta domin ceto rayukan iyaye mata da jariran da su ke dauke da su, ganin yadda ake asarar rayuka da dama sabili da rashin biyan kudin kula da su.

Saurari cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Tsadar Rayuwa Na Hana Mutane Zuwa Asibiti