A yau talata, mambobin kungiyar kwadago ta NLC suka kutsa kai cikin ginin Majalisar Tarayyar Najeriya dake Abuja a ci gaba da zanga-zangar da suke yi game tsadar rayuwa a kasar.
Washington DC —
Masu zanga-zangar na dauke da kwalaye masu mabambantan sakonni a rubuce, sun isa harabar majalisar da misalin karfe 10 na safiya.
Sabanin yadda aka saba gani a baya, a wannan karon kofofin shiga majalisar sun kasance a bude, inda masu zanga-zangar suka shiga ba tare da fuskantar turjiya daga jami’an tsaro ba.
Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero ya ce manufar gudanar da zanga-zanga a fadin kasar ita ce sanar da Shugaban Kasa Bola Tinubu game da halin kuncin da ‘yan Najeriya ke ciki.
A cewarsa, al’amarin bai takaita ga muradan NLC ba kawai harma da irin yunwar da ake fama da ita a Najeriya