Gwamnatin Najeriya za ta bada talakawan wasu jahohi 12 tallafi, ta hannun gwamnatocin jahohin, a cigaba da tsarin bada albashi ga masu sana'o'in hannu da gwamnatin ta fara a watan Satumban bana. Ya zuwa yanzu dai jihohi 12 masu dubban mutanen da ke da kananan sana'o'i suka amfana a karon farko daga cikin Naira biliyan 75 da aka ware.
Shirin tallafin da ta ke bayarwa ta hannun gwamnatocin jihohi, na daga cikin wata hikima da gwamnatin ta Najeriya ta 6ullo da ita domin karfafa gwiwar masu kananan sana'o'i don su yi dogaro da kansu su kuma samar da ayyukan yi ga yan'uwansu matasa masu neman aiki.
Wadannan Kudade ne da gwamnatin Najeriya ta ware, ta yadda shirin zai samu nasara da ya kamata a cewar Ministar Masana'antu Maryam Yelwaji Katagum. Ranar Litinin mai zuwa ne za a fara biyan jihohi 12 don amfanar talakawansu, kama daga masu keke Nafep da babura da direbobi masu motocin kansu. Yelwaji ta ce kowani mai sana'ar hannu na iya samun wannan kudi da Gwamnati ta ce a bada su kyauta.
Amma wani mai masana'anta dake jihar Kano, Habibu Lawal Kofar Wambai ya koka cewa ba dukan masu masana'antu da kananan sana'o'i ne sukan san wannan batu na tallafi ba, saboda haka yake kira ga gwamnatoci tun daga kananan hukumomi da na Jihohi da ma na gwamnatin tarayya da su yi amfani da kafafen yada labarai wajen fadakar da mutane akan wanan tallafi domin a baya sun dan samu matsaloli a lokacin shirin gwamnati na You-WiN.
A halin yanzu kamfanoni dubu 26 sun riga sun amfana, inda aka biya ma'aikatansu dubu dari da daya da suka riga suka samu kudadensu kai tsaye.
Ga Madina Dauda da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5