Trump Ya Zargi McCabe, Rosenstein Da Cin Amanar Kasa

Andrew McCabe

McCabe ya ce mai yiwuwa Trump ya aikata wani babban laifi, lokacin da ya kori Shugaban hukumar bincike ta FBI James Comey a watan Mayu na 2017, a lokacin Comey na jagorantar binciken alakar kwamitin yakin neman zaben Trump da kasar Rasha, game da zaben Shugaban kasar Amurka na 2016.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce wasu jiga-jigan jami’an tsaro sun ci amanar kasa, lokacin da su ka kwatanta yin amfani da wani gyara a 2017 ta Kudin Tsarin Mulki wajen tsige shi, a yayin da kuma su ke shirin fara bincikensa kan yiwuwar ya yi karan tsaye ga shari’a.

Trump, wanda a lokacin ya ke wurin shakatawarsa na Mar-a-Lago da ke gabar ruwa a jihar Florida, ya caccaki tsohon mukaddashin Hukumar Bincike ta FBI Andrew McCabe, wanda ya gaya ma wani shirin gidan talabijin na CBS News mai suna 60 Minutes na daren Lahadi.

McCabe ya ce, da shi da Mataimakin Attoni-Janar din Amurka Rod Rosenstein sun tattauna kan yiwuwar amfani da gyaran na 25 ta kundin tsarin mulki, wadda ta amince Mataimakin Shugaban kasa da 15 daga cikin mambobin majalisar zartaswar kasa, su ayyana Shugaban kasa a matsayin wanda ba zai iya gudanar da ayyukansa ba.

Wanda hakan zai sa Mataimakin Shugaban kasa zama mukaddashin Shugaban kasa.