A cikin kalaman da ya rubuta akan shafinsa na Twitter, Trump ya ce “zai yi kyau idan China ta taimaka mana wajen shawo kan wannan matsalar, in kuma ba ta yi ba, mu za mu magance matsalar da kanmu.”
Sai dai Trump bai fayyace irin matakan da Amurkan za ta dauka wajen warware matsalar ta Korea ta Arewa ba.
Haka kuma ya ce ya shaida wa shugaban China, Xi Jinping a taron kolin da suka yi a cikin makon jiya cewa China za ta fi samun damar cin moriyar yarjeniyoyin cinikayyar da take neman kullawa da Amurka idan China din ta taimaka wajen “warware wannan matsalar ta.”
China dai ita ce babbar kasar da Korea ta Arewa ta dogara akanta fiye da kowace kasa a duniya, abin da ya sa har Cibiyar Nazarin Harkokin Waje ta Duniya take bayyana China a matsayin kasar da Koriya din ta dogara akanta wajen samun ci gaba a harkokinta na kasuwanci da makamai da abinci.