Trump Ya Zake Kan Gina Katanga A Kan Iyakar Amurka Da Mekziko

Yayin da wasu ma'aikatun gwamnatin tarayyar Amurka ke cigaba da zama a rufe sanadiyyar takaddama kan batun gina katanga akan iyakar Amurka da Mekziko, Shugaba Donald Trump ya tsaya kai da fata sai an samar da kudin gina katangar.

Shugaban Amurka Donald Trump ya zake kan bukatarsa ta gina katanga a kan iyakar Amurka da Mexico. A yayin da 'yan Dimokarat kuma ke cigaba da kin goyon bayan abin da su ke kira mataki mai tsada da kuma rashin inganci.

Yau dinnan Litini, aka shiga rana ta 24 da rufe wasu ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Da daren jiya Lahadi Trump ya yi rubuce-rubuce a shafinsa na twitter, inda ya ambaci maganan wani dan ra’ayin rikau Pat Buchanan; inda Buchanan ya yi kira ga Trump ya yi amfani da ikonsa na Shugaban kasa, ya kafa dokar ta baci dan ya sami kudin gina katangar.

Sai Trump ya dora akai da nasa bayanin cewa, “‘Shahararrun mutanen kasarmu na bukatar cikakken tsaro a kan iyakarmu yanzun nan!"

Jiya Lahadi, wani aminin Trump daga cikin 'yan majalisar dattawan Amurka ya yi kira gare shi da ya bude ma'aikatun a kalla na wuccin gadi sannan ya sake gwada tattaunawa da 'yan Dimokarat.