Trump Ya Yi Dokar Da Za Ta Sa Ido Kan Kafafen Sada Zumunta

Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wani umurni na gashin-kansa wanda ya ce zai saita yadda ake amfani da kafafen sada zumunta.

Sai dai masu fashin baki na ganin abu ne mai kamar wuya wannan doka ta yi tasiri musamman idan aka kalle ta a shari’ance.

Trump ya ce ya samar da dokar ce, saboda “a kare ‘yancin fadin albarkacin baki da Amurkawa ke da shi.”

A dai jiya Alhamis Trump ya fadawa manema labarai a ofishinsa cewa, a da kafafen sada zumunta suna da kariya, “amma sanadiyyar wannan doka, ba za su samu wannan kariya ba."

Shi dai wannan umarni zai bukaci hukumar da ke sa ido kan kafafen yada labarai, ta fayyace wani sashi da ya shafi dokar sanin ya kamata, wanda a lokuta da dama bai cika shafar kafafen sada zumunta na yanar gizo ba – wanda hakan kan ba su damar kaucewa rikicin yiwuwar a maka su a kotu kan batutuwan da suka shafi bayanan da masu bibiyarsu ke wallafawa.

Umurnin har ila yau, ya ba ofishin da ke sa ido kan bangaren da ke kula da tsare-tsaren kafafen yanar gizo a fadar White House, damar ya tattaro korafe-korafen da ake yi kan yadda ake tace bayanai, ya kuma mika su ga hukumar da ke kula da harkokin cinikayya da ma’aikatar shari’ar kasar.

Da yawa dai na kallon wannan sabuwar doka da Trump ya rattaba a hannun akai, a matsayin martani ga kamfanin Twitter, wanda a farkon makon nan ya bukaci masu bibiyan shafin da su yi hattara da sahihancin wasu bayanai da Trump ya wallafawa a shafinsa na Twitter, gargadin da wasu ke ganin bai yi wa Trump dadi ba.