Trump ya shiga shafinsa na Twitter da sanyin safiyar yau inda “a baya an yi kokarin a nuna akwai alaka tsakanina da Rasha, amma babu hujja, yanzu kuma an kirkiro batun cewa na hana doka ta yi aikinta.”
A wani sakon Twitter na biyu kuma, Trump ya ce “mutane suna shaida bita-da-kullin-siyasa mafi girma a tarihin siyasar Amurka, wanda wasu bata-gari ke jagoranta.”
Shugaban na Amurka ya maida wannan martani ne bayan da rahotanni a jiya Laraba suka nuna cewa Lauya na musamman Robert Mueller na shirin yin hira da wasu manyan jami’an tsaron kasar, kan bukatar da Trump ya gabatar na a yi watsi da binciken alakar tsohon mai ba shi sharawa kan harkar tsaro Michael Flynn da jakadan Rasha dake Amurka.
A watan Fabrairun Trump ya sallami Flynn daga aiki bayan da ya kwashe kwanaki 24 kacal ya na rike da mukamin.
Hakan ta faru ne bayan da Trump ya gano cewa Flynn ya yi wa mataimakin shugaban kasar Mike Pence karya kan tattaunawar da suka yi da jakadan na Rasha Sergey Kislyak.