Trump Ya Shigar Da Wata Kara Akan Shari'ar Yunkurin Sauya Sakamakon Zabe

Trump Hush Money

Tsohon shugaba Trump, kuma dan takarar jami’iyar Republican a zaben 5 ga watan Nuwamban 2024, ya ajiye damarsa ta bayyana a gaban kotu, kana maimakon haka ya umarci lauyoyin sa su shigar da karar a madadin sa.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya fada a wata karar da ya shigar a kotu jiya Talata cewa ba zai amince da zargin aikata laifi ba a shari’ar da aka sake tayar da shi, inda aka same shi da laifin yunkurin sauya sakamakon zaben da ya fadi a 2020.

Tsohon shugaba Trump, kuma dan takarar jami’iyar Republican a zaben 5 ga watan Nuwamban 2024, ya ajiye damarsa ta bayyana a gaban kotu, kana maimakon haka ya umarci lauyoyin sa su shigar da karar a madadin sa.

Batun samun shi da laifin da aka sake tayarwa, wanda lauya na musamman Jack Smith ya samo a makon da ya gabata, ya hada da wasu tuhume-tuhume guda hudu da masu gabatar da kara suka yi wa Trump a bara. An zarge shi da yunkurin damfarar Amurka, tare da hana majalisa tabbatar da sakamakon zabe da kuma hana masu kada kuri'a damar yin zabe na gaskiya.

An jingine sabuwar tuhumar sannan aka sake fasalin wasu zargi bayan da kotun kolin Amurka ta yanke hukuncin cewa Trump na da babbar kariyar dage tuhuma kan ayyukan jami’an da ya dauka a matsayinsa na shugaban kasa.

An shirya da masu gabatar da karar da lauyoyin Trump zasu bayyana a gaban kotu a ranar Alhamis domin sanin mataki na gaba bayan hukuncin kotun koli a kan kariyar da Trump ke da ita.