Trump Ya Sauya Matsaya Kan Dakatar Da Kwamitin COVID-19

Shugaban Amurka Donald Trump ya sauya matsayarsa yanzu ya ce zai bar kwamitin da ya nada don yaki da annobar coronavirus har zuwa wani lokaci da ba shi da wa’adi, amma ya ce zai mayar da manufofinsa su zama sun karkata wajen kare lafiyar Amurkawa tare da bude tattalin arzikin kasar.

Shugaban da mataimakinsa Mike Pence wanda ya jima yana sanya ido kan yadda Amurka ke yaki da cutar corononavirus ya ce kwamitin da aka nada kan cutar zai daina aiki a karshen watan Mayu ko kuma a farkon watan Yuni.

Amma bayan da wasu masu adawa da hakan suka soki matsayar shugaban akan wannan lamarin, a jiya Laraba Shugaba Trump ya shiga shafinsa na twitter inda ya ce ba za a soke kwamitin ba, sai dai kwamitin zai mayar da hankali kan tabbatar da lafiyar Amurkawa da kuma yadda za a bude kasar.

A ranar Talata ne shugaban ya ce a ganinsa lokaci ya yi da ya kamata a bude tattalin arzikin Amurka, wanda ke kan gaba a duniya.

Tattalin arzikin kasar dai ya fuskanci koma baya tun farkon bullar wannan cutar, haka kuma mutune miliyan 30 sun rasa ayyukansu.