Trump Ya Sassauta Kalamansa A Kan Mexico

Shugaba Trump

Shugaba Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya aike da wani sakon Twitter da yammacin jiya Juma’a yana yabawa Mexico kana ya yiwa Canada barazana.

Sakon Twitter Trump yana cikin kokarin da shugaban ke yin a sake tattaunawa a kan shirin cinikayya na kasashen nahiyar Arewacin Amurka ko kuma NAFTA.

Kalaman na shi ga Mexico na da sassauci, wani lamari da ba a saba ji daga bakin Trump a kan yan kasar Mexico da ma Mexico dan kanta. A laokcin yakin neman zabensa, Trump ya lashi takobin sai ya tilastawa Mexico ta biya kudin gina Katanga tsakanin kasashen biyu, lamarin da ya gaza cimma tun hawarsa mulki. Ya kuma kwatanta yan Mexico da masu fyade a lokacin kempensa.

Trump yace harkoki tare da Mexico na yin inganci. Yace a rika kula da ma’aikatan kamfanin kera motoci da manoma ko kuma ba za a ci gaba da hulda ba.

Shugaban na Amurka ya yi kalamai masu dadi ga sabon shugaban Mexico mai jiran gado Andres Manuel Lopez Obrador, wanda zai fara aiki a matsayin shugaban kasar a cikin watan Disemba. Yace sabon shugaban na Mexico cikakken dattijo ne.

Sai dai kalaman na Trump sun canza a kan kasar Canada, yana mai cewar Canada ta saurara. Yace haraji da shingaye cinikayya da ta take sanya sun yi tsanani.