Shugaban Amurka Donald Trump ya sa ala tilas Shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi ta soke wata ziyara ta shirya kai wa kasashen Afghanistan da Brussels jiya Alhamis.
Wannan ita ce sabuwar takaddamar da ta kunno kai tsakanin manyan 'yan siyasar biyu bayan rufe ma’aikatun gwamnati mafi tsawo da aka yi a tarihin Amurka.
A wata wasikar da ya aika wa Shugabar majalisar wakilan, Trump ya hana Pelosi da sauran ‘yan Majalisar wakilai amfani da jirgin sojojin kasar don tafiya su gana da kawayen Amurka a kungiyar kawance ta NATO a Brussels da kuma sojojin Amurka a Afghanistan.
A cewar Trump, “kasancewar ma’aikatan gwamnatin Amurka ba su samun albashi, na tabbata cewa jinkirta wannan tafiya shi ya fi dacewa.”
Mai magana a madadin ofishin Pelosi ya ce wannan ziyarar, da an yi ta, da ta “bayar da damar yin muhimman jawabai kan matsayin kasar game da wasu batutuwa na tsaro” da kuma ta zama wata dama ga Pelosi ta gode ma sojojin.
Wasikar da shugaban kasa ya tura ma Pelosi ba ta yi magana kai tsaye kan kiran da Pelosi ta yi ma shugaban kasa cewa ya jinkirta jawabi kan makomar kasar, wato "State of the Union Address," a ranar 29 ga wata har sai an samar da kudin gudanar da gwamnati kuma an kawo karshen rufe wasu daga cikin ma’aikatun gwamnati.