Trump Ya Raina Zabin Biden

Shugaban Amurka Donald Trump ya kwatanta Kamala Harris da Joe Biden ya zaba ta zama mataimakiyarsa, a matsayin “irin abokiyar hamayyar da kowa yake muradin ya samu.”

“Kamala Harris ta fara da karfinta a zaben fidda gwani na ‘yan Democrat, amma ta kammala a matsayin mai rauni.” Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Shi dai Biden shi ake kyautata zaton zai tsayawa jam'iyyar Democrat takara a zaben shugaban kasar.

Bayan da Biden ya zabi Harris a jiya Talata, Trump ya ce ya yi mamakin cewa ita Biden ya zaba a matsayin mataimakiyar shugaban kasa, inda ya kuma kwatanta yunkurin da ta yi na neman takararar shugaban kasa a matsayin gazawa.

“Na yi mamaki sosai saboda yadda ta kare ba tare da ta tabuka komai ba…. a zaben fidda gwani,” Trump ya ce a taron manema labarai da aka yi a fadar White House a jiya Talata

Shugaba Trump ya kuma zargi Harris da kasancewa “mara kara” ga Brett Kavanaugh, alkalin da Trump ya zaba a kotun kolin kasar, kan yadda ta tambaye shi zargin da ake masa na lalata a shekarar 2018, a lokacin da ake zaman tantance shi a majalisa.

A dai jiya Talata ne tsohon mataimakin shugaban kasa Biden ya zabi Harris a matsayin abokiyar takararsa bayan da aka kwashe tsawon lokacin ana tantance mata da dama da ake ganin zai zaba daga cikinsu.

A ranar 3 ga watan Nuwamba Amurkawa za su yi zaben shugaban kasa, inda shugaba Trump zai nemi wa'adi na biyu.