Bayan da Rasha ta tura dakarunta zuwa kasar Venezuela, Shugaban Amurka Donald Trump ya aikawa da Rashan wani gargadi
“Ya zama dole Rasha ta fice.” Inji shugaba Trump.
Shugaban na Amurka ya yi wannan furuci ce ne, yayin da yake ganawa da manema labarai a Fadar White House a jiya Laraba, a lokacin da yake karbar bakuncin uwargidan shugaban ‘yan adawan kasar ta Venezuela, Fabiana Rosales.
A lokacin da manema labarai suka tambayi Trump ko yana duba yiwuwar shi ma ya tura dakarun Amurkan zuwa kasar ta Venezuela sai ya ce, “Amurka za ta iya amfani da kowanne irin zabi.”
Yayin da take na ta jawabin, uwargidan Juan Guaido, wacce ta shiga har cikin ofishin shugaban kasa na Oval Office, ta ce jama’ar kasar ta Venezuela na cikin mawuyacin hali na rayuwa, musamman ma kananan yara.