A yau Talata ne wakilai daga kasashen biyu, wadanda a hukumance har yanzu suna cikin halin yaki da juna, zasu gana a kauyen Panmunjob, wanda ake kira kauyen zaman lafiya dake kan iyakar kasashen biyu, kuma inda aka rattaba hannu a yarjejeniyar sulhu ta shekarar 1953 wadda ta kawo karshen fada a tsakanin kasashen biyu.
A jawabinsa na sabuwar shekara, shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, ya ce zai aika da ‘yan wasan kasarsa zuwa gasar wasannin Olympics zuwa Koriya ta Kudu, jim kadan bayan da yayi barazanar cewa yana da madannin makaman nukiliya akan teburin ofishinsa, da zai iya harbawa zuwa Amurka.
Shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in, wanda ke neman sasantawa da Koriya ta Arewa, ya mayar da martani ta hanyar mika goron gayyatar tattaunawa ga gwamnatin Kim.
Tattaunawar da za a yi yau Talata, ana kyautata tsammanin zata mayar da hankaline kan gasar Olympics, da kuma ko ‘yan wasan Koriyoyin biyu zasu yi tattaki tareda juna a lokacin shagulgullan bude gasar.
Za kuma a iya shigar da wasu batutuwa ciki kamar dawo da shirin hada iyalan kasashen biyu da kuma yadda za a inganta dangantakar kasashen biyu.
Babu hannun Amurka a cikin tattaunawar da za ayi ta yau Talata.