Trump Ya Kaddamar Da Yakin Neman Zabensa Na 2020

Yayin da yakin neman zaben Shugaban kasar Amurka na 2020 ke dada kankama, Shugaban Amurka Donald Trump ya kaddamar da yakin neman zabensa gaban cincirindon magoya bayansa, inda ya tabo wasu batutuwa masu sarkakkiya baya ga shagube da ya yi ta yi na burge magoya bayansa.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kaddamar da yakin neman zabensa a karo na biyu a wani gangami a birnin Orlando na jihar Florida, ‘daya daga cikin muhimman jihohin da suka taimaka masa yin nasara a zaben shekarar 2016.

Mahalarta gangamin sun yi masa maraba ta hanyar fadin “USA” abin da ya tuna masa da yadda ya fara yakin neman zabe shekaru hudu da suka gabata.

Shugaban kasar ya ce “ta kasance fiye ma da wani gawurtaccen yakin neman zabe. Ta kasance wani tsarin siyasa mai kyau saboda ku,” a cewar Trump lokacin da yake fadin sakonsa iri ‘daya da na farkon lokacin da ya fara tsayawa takarar shugaban kasa. Ya ci gaba da cewa “wannan wani sauyi ne da mutane suka fara…. Wadanda suka yi imanin cewa dole sai ‘kasa ta fara kula da ‘yan kasarta da farko.”

Ya yin da yake tallata batutuwa irinsu tattalin arziki da tsaron iyakar kasa, shuguaban kasar kuma ya soko abokin takararsa a matsayin mai ra’ayin ‘yan gurguzu da ra’ayin gaba dai gaba dai wanda suke kokarin ganin sun bata shi da iyalansa, haka kuma suna yi masa kallon kaskanci shi da magoya bayansa.

Shugaba Trump, ya yin da yake jawabi, ya kira wasu daga cikin kafafen yada labaren Amurka da cewa makaryata ne.

Ga cikakken Tattaunawar:

Your browser doesn’t support HTML5

Trump Ya Kaddamar Da Yakin Neman Zabensa Na 2020