Trump Ya Je McDonald's Ya Yi Aiki

Trump a lokacin da yake zuba soyayyan dankali ga wani kwastoma

Ziyarar da Trump ya kai fitaccen shagon sayar da abincin na zuwa ne yayin da yake jaddada ikirarin da yake yi ba tare da gabatar da wata hujja ba cewa  ‘yar takarar jam’iyyar Democrat Kamala Harris ba ta taba yin aiki a McDonald's ba a lokacin da take karatu a kwaleji.

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican, Donald Trump, ya yi aiki a wurin sayar da abinci na McDonald's a Pennsylvania.

Ziyarar da tsohon shugaban kasar na Amurka ya kai wurin sayar da abinci na zuwa ne kafin ya shirya wani taron manema labarai da ya yi na bazata.

Trump ya amsa tambayoyi daga 'yan jarida ta taga da ake biya tare da karbar abinci a mota.

Trump yana mikawa wani kwastoma abinci a McDonald

Wani ma’aikaci a wurin ya nuna wa Trump yadda ake soya dankali, har ma ya rika taimakawa wajen mikawa kwastomomi abincinsu ta taga.

Ziyarar da Trump ya kai fitaccen shagon sayar da abincin na zuwa ne yayin da yake jaddada ikirarin da yake yi ba tare da gabatar da wata hujja ba cewa ‘yar takarar jam’iyyar Democrat Kamala Harris ba ta taba yin aiki a McDonald's ba a lokacin da take karatu a kwaleji.

A lokacin da Trump yake aikin a McDonald's an hana kwastomomi shiga saboda dalilai na tsaro.