Trump Ya Jaddada Aniyarsa Ta Gina Katanga Tsakanin Amurka da Mexico

Donald Trump

Dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar Republicans a zaben da za’ayi na wannan shekara a nan Amurka, Donald Trump ya sake jadadda matsayinsa na cewa zai kori dukkan ‘yan cin-ranin dake zaune ba bisa ka’ida ba dake cikin kasar, in ya ci zaben.

Sai dai masu nazari sun lura da cewa akwai banbanci tsakanin lafazi mai tsanani da yayi anfani da shi jiya Laraba wajen jadadda wannan matsayin (a lokacinda yake jawabi ga magoya bayansa a jihar Arizona ta nan Amurka), da kuma lafazin da yayi anfani da shi lokacinda ya ziyarci kasar Mexico inda aka ce yayi magana da lafazi mai laushi kuma a natse a lokacin ganawarsa da shugaban Mexico din, Enrique Pena Nieto.

Wani banbanci da ake gani shine yadda Trump ke nuna alamun canja matsayinsa gameda gina wani makeken shinge tsakanin Amurka da Mexico don hana mutane tsallakowa suna shigowa Amurka.

Trump yace a lokacin ganawarsa da shugaban Mexico din, sun zanta kan maganar gina katangar amma ba suyi maganar wanda zai biya kudaden aikin ba. To amma shi shugaban na Mexico yace ya gayawa Trump kai tsaye cewa Mexico ba zata biya ko sisin kwabo ba wajen girka wannan katangar.