Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Ya Ce Wajibi Ne Gwamnatin Sa Ta Yi Waje Da Wadanda Suka Shiga Kasar Ta Barauniyar Hanya


Dan takarar Shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump, ya fadi jiya Laraba cewa a gwamnatinsa, babu yadda za a yi wadanda su ka shigo Amurka a sace su zama 'yan kasa.

Ya yi bayani sosai game da manufofinsa kan shigowar baki ga taron magoya bayansa, a jahar Arizona ta kudu maso yammacin Amurka, bayan ganawarsa da Shugaban Mexico Enrique Pena Nieto.

Da farko ya jaddada aniyarsa ta gina katanga tsakanin Amurka da Mexico, ya ce kuma wai kasar ta Mexico ce za ta biya kudin, duk kuwa da nanatawar da Shugaba Pena Nieto ya yi cewa gwamnatinsa ba za ta biya ba.

"Yanzu ba su sani ba tukun, amma lallai su za su biya kudin gina katangar." in ji shi.

Trump ya ce Amurka na da damar zakulo baki wadanda, ga dukkan alamu, za su iya yin fice su shahara, su kuma kaunaci Amurkawa.

"Kuma dole mu fuskanci gaskiya, kan abin da ya ke tabbas, cewa ba kowani mai son shiga kasarmu zai iya sajewa da mu ba."

Trump ya bayyana manufofinsa game da kaurar bakin da cewa, sun fi raja'a ne kan bukatar inganta tsaro da kuma tattalin arzikin Amurkawa, ya kuma ce shirin zai rage yawan aikata manyan laifuka, da kungiyoyin miyagu, da kwararowar bakin haure da kuma dogaro ga tallafin gwamnati.

"Mutane za su san cewa, ba za ka sadado ciki kawai, ka labe ka na jiran a maida kai dan kasa ba," in ji shi.

To amma Trump ya fi lafawa a wani taron manema labarai a Mexico City, bayan ganawarsa da Shugaban Mexico, wanda ya bayyana da mai muhimmanci kuma na keke-da-keke.

"Ina kaunar Amurka sosai kuma ina son inga mutanen Amurka sun samu kariya sosai," a cewar Trump ga Pena Nieto. Ya kara da cewa, "Kai ma ai ka bayyana yadda ka ke ji da kuma kaunarka ga kasarka ta Mexico."

XS
SM
MD
LG