Donald Trump ya iso nan birnin Washington DC da daren jiya Assabar don fara bikin rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Amurka karo na biyu.
Trump ya baro jiharsa ta haihuwa ta Florida da yammacin jiya Assabar tare da matarsa Melania da dansa Barron, don tashi zuwa babban birnin kasar.
Zai halarci wata liyafar maraice da wasan wuta a gidan wasan Golf na Trump a Sterling ta jihar Virginia.
A yau Lahadi an tsara Trump zai halarci bikin shimfida furanni a makabartar Arlington, kafin ya nufi wani gangami a dandalin Capital One Arena da ke Washington.
A ranar Litinin, za a rantsar da shi a cikin ginin majalisar dokoki ta Capitol saboda yanayin sanyi.
A halin da ake ciki kuma sauya tsarin bikin rantsar da zababben shugaban zuwa cikin daki saboda tsananin sanyi da ake sa ran za’a yi, zai sa akasarin bakin da suke da tikiti ba za su sami damar halartar bikin a zahirance ba.
Kwamitin gudanar da bikin ya ce "Wadanda ke da tikitin manyan bakin shugaban kasa da kuma 'yan majalisar dokoki za su sami halarta da kansu." Amma kuma ya ce "mafi yawan baƙi masu tikitin ba za su iya halartar bukukuwan da kansu ba."
Kwamitin ya “shawarci jama’ar da suka hallara a Washington don su shaidi taron, da su je a wuraren kallo na cikin dakuna da aka tanada domin kallon bikin.”
An yi hasashen samun sanyi mai tsanani a ranar bikin rantsarwar, inda ake sa ran yanayin zafi a babban birnin Amurka zai yi kasa da digiri 11 bayan sifili, wato -11 a ma'aunin Celsius.
Akasarin baki sama da 220,000 masu tikitin da suka kuduri aniyar shaidar bikin a harabar ginin majalisar dokoki na US Capitol, ba za su sami damar ganin rantsar da Trump kai tsaye ba.
Rundunar ‘yan sandan Capitol ta Amurka ta fada a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, za'a rufe wuraren da aka tanadar wa baki masu tikiti da ke fuskar yammacin ginin na Capitol a gobe Litinin.