Trump Ya Fara Tunanin Waiwayar Tsirarun Amurka

Bayan da aka kwashe makonni ana zanga-zanga a Amurka, Shugaba Donald Trump ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta tashi tsaye wajen bunkasa tattalin arzikin unguwannin tsirarun al’ummar kasar, ya kuma tunkari bambancin da ake da shi a fannin kiwon lafiya a wuraren.

Fadar White House, ba tare da bada cikakken bayani ba, ta ce, wannan na zaman wani bangare na tsarin wasu shirye-shirye guda hudu "na kare jama’ar, da ba su dama, da kuma mutuntasu."

Da ya ke jawabi a jiya Alhamis a wani taro game da wariyar launin fata da kuma batun ‘yan sanda a wata majami'a da ke Dallas, a jihar Texas, Shugaban ya ce a matsayin wani bangare na shirin, zai rattaba hannu kan wata doka, wadda za ta bukaci ‘yan sanda su kiyaye ka'idodin kwarewa wajen amfani da karfi.

Trump ya kuma yi watsi da sukar da aka yi masa akan kalaman da ya yi a baya game da bukatar jami’an tsaro su mamaye tituna a daidai lokacin da ake zanga-zanaga da tashin hankali a kasar.