Shugaban Amurka Donald Trump ya dakatar da ba da takardun biza da ake ba baki domin zuwa su yi aiki a nan Amurka har sai zuwa nan da karshen shekarar nan.
A cewar Trump, daukan matakin ya zama dole domin hakan zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasar da ya shiga mawuyacin hali sanadiyyar cutar coronavirus da ayyukan da Amurkawa suka rasa.
Matakin ya shafi rukunan biza na H-1B da kamfanoni da suka hada da na kere-kere suke amfani da ita wajen daukan ma’aikata da bizar J-1 da ake amfani da ita wajen musayar dalibai sai kuma bizar L-1 ta daukan manajojin manyan-mnayan kamfanoni a nan Amurka.
Umurnin na wucin gadi wanda shugaba Trump ya rattaba hannun akai a jiya Litinin ya hada har da bizar H-2B wacce ma’aikata ke amfani da ita wajen yin aiki lokaci-zuwa-lokaci a nan Amurka a fannin da bai shafi ayyukan noma ba.
Ko da yake, wannan rukunin bizar bai shaft wadanda ke aiki a fannin sarrafa abinci ba, da ma’aikatan lafiya da kuma masu ayyukan raino da noma.
Ana yi hasashen wannan mataki da gwamnatin ta Trump ta dauka zai hana ma’aikata ‘yan kasar waje dubu dari 525 ayyana kansu a matsayin wadanda ba su da aikin yi a Amurka.