Shugaban Amurka Donald Trump ya ce an fasa wani zaman tattaunawa da aka shirya za a yi a yau Lahadi tsakanin shugaban Afghanistan Ashraf Gani da gaggan shugabannin kungiyar Taliban a wurin shakatawarsa da ake kira Camp David da ke jihar Maryland, wacce ba ta da nisa da birnin Washington DC.
Cikin wasu sakonnin Twitter da ya wallafa da yammacin jiya Asabar, Shugaba Trump ya ce an fasa zaman ne bayan wani harin bam da aka kai a cikin wata mota a Kabul, wanda ya halaka mutum 12, ciki har da wani sojan Amurka.
Trump ya ce idan dai har kungiyar ta Taliban ba za ta tsagaita-wuta ba a wannan muhimmin lokaci da ake zaman sulhu, har su kashe mutum 12 da ba-su-ji-ba-su-gani-ba, hakan manuniya ce cewa ba su da karfin ikon da za a cimma wata matsaya da su.
An dai kwashe watannin ana ta laluben bakin zaren yadda za a kawo karshen yakin na Afghanistan, tsakanin jami’an diplomasiyyan Amurka da na Taliban, wadanda suka ki amincewa da wani shirin tsagaita-wuta.