Shugaba Donald Trump na Amurka yau ya gayawa mahalarta taron tattalin azriki na duniya da ake a birnin Davos na Switzerland cewa kullum muradun Amurka ne zai sa a gaba, amma wannan ba wai yana nufin Amurka din ba zata yi aiki tare da sauran kasashen duniya ba.
Trump ya kuma yi hasashen cewa tattalin arzikin Amurka ne zai zama direban jan motar tattalin arzikin sauran kasashen duniya, tare da cewa kullum abinda zai amfani Amurka ne a gabansa kamar yadda ya kamata su ma sauran shugabannin kasashen duniya su ba wa nasu kasashen muhimmanci.
Tun ma kafin yayi jawabin, shugaban na Amurka yayi kokarin yin maslaha da Shugaba Paul Kagame na Rwanda, wanda kuma shine shugaban Kungiyar Kasashen Afirka ta AU.
Musamman ma dangane da kalamin batancin da shi Trump din da ya yiwa kasashen Afirka kwannakin baya, inda ya kira su da kaskantattu kamar ramin shadda.
A haduwar da suka yi, Trump ya nemi Kagame da ya isarwa Afirkawa da kyakyawan fatansa na alheri ga kasashen na Afirka.