Shugaban Amurka Donald Trump, ya canza shugaban ma'aikata a fadar White, Reince Priebus. Wanda ya maye gurbin shine Janar John Kelly mai ritaya, wanda kamin wannan canji, shine ministan ma'aikatar tsaron cikin gida ta Amurka.
A makonnin baya bayan nan dai shugaba Donald Trump yana maida Priebus tamkar saniyar ware, ta kai ga sabon Darektan yada Labarai a fadar White House Anthony Scrammuci, ya ambaci Priebus din a zaman mutum "wanda yake da tabuwa".
Da take magana da manema labarai a maraicen Jumma'a, sakatariyar yada Labarai a fadar White House, Sarah Huchabee Sanders, tace "tun mako biyu da suka wuce ne, shugaba Trump da Reince Priebus, suka fara tattaunawa kan wannan canji".
A hira da yayi da tashar talabijin ta CNN bayan da yayi murabus, Priebus yace, "shugaban na Amurka yana so ya kawo canji."
" Ina ji lokaci yayi domin sauya fasali," in ji Priebus. Abu ne da a ganina fadar ta White take bukata."
Priebus yace gaskiyar magana, tun ranar Alhamis ya mika takardar sa ta murabus, amma sai jumma'a, aka bayyana ta.