Trump Ya Caccaki 'Yan Demokrat Akan Gayyatar Mueller

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ji dadin bayanin da tsohon mai bincike na musamman, Robert Mueller yayi a lokacin da ya bayyana a gaban wasu kwamitoci na majalisar wakilan Amurka guda biyu.

Yana mai cewa shi da sauran ‘yan jam’iyyar sa ta Republican sun "ji dadin ranar" shugabar majalisar wakilai Nancy Pelosi, ta ce bayan bayanin da Mueller yayi game da binciken yiwuwar Rasha ta yi katsalanda a zaben Amurka, na shekarar 2016 da kuma zargin Trump ya hana shari’a ta yi aikin ta, 'yan jam'iyyar Democrat zasu ci gaba da gudanar da na su binciken akan shugaban da gwamnatinsa.

Trump da ‘yan jam’iyyar Republican a majalisar dokokin kasar sun sha caccakar ‘yan Democrat dake majalisar wakilan kasar, akan gayyatar Mueller ya bada bahasi a gaban kwamitin binciken bayanan sirri da na shari’a, yana mai cewa bai kamata su ci gaba da wannan binciken ba.

Amma maganganun da shugabannin majalisar wakilan kasar suka yi bayan zaman jin bahasin, na nuna alamun suna da niyyar su ci gaba da maida hankali akan fadar White House, ciki harda yiwuwar fara shirin tsige shugaban nan gaba idan suka sami kwararan hujjoji da kuma goyon bayan jama’a.