Duk da cewa tattaunawar su ta lalace a Vietnam a cikin makon nan, da alamu shugaban Amurka Donald Trump bai dauki wani abu da zafi ba akan shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un, tun da ya kira shi “shugaban kwarai”.
A wata hira da Sean Hannity na gidan talabijin din Fox News yi da shi a birnin Hanoi, wadda aka nuna a talabijin a daren jiya Alhamis, Trump ya bayyana Kim a matsayin “mutum mai zurfin tunani wanda kuma ba aka iya cewa ga inda zai dosa.”
Trump ya kuma fadi cewa Kim na burge shi haka kuma shi ma Kim din Trump na burge shi. “Wasu mutane na cewa haba, bai kamata ya burge ka ba.” Na ce masu don me ba zai burge ni ba.” a cewar Trump. Shugaban ya kuma fadi cewa su duka biyun suna samun fahimtar juna.
An shirya liyafar rana ta manyan mutane a katafaren otel din Metropole, an kuma shirya wani biki don sanya hannun da shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Korea ta arewa Kim Jong Un zasu yi a wasu yarjeniyoyi. Amma kuma cikin gaggawa aka soke duka bukukuwan biyu kafin jiya Alhamis, abinda ya kawo karshen taron kolin na biyu tsakanin shugabannin manyan kasashen biyu ba tare da shiri ba.