Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ya yi wata tattaunawa mai ma’ana ta wayar talho da takwaran aikinsa na China Xi Jingping, yana mai cewa suna shirin wata tattaunawa mai fadi, kan harkokin cinikayya a mako mai zuwa.
Ana sa ran shugabanin biyu da za su hadu a taron kasashe 20 da suka fi karfin tattalin arziki a duniya na G20, wanda za a yi a Japan.
Kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ruwaito Shugaba Xi yana cewa, ya jaddadawa Trump muhimmanci su tattauna a mataki na bai-daya, inda ya kara da cewa, yin takaddama da juna ba ita ce masalaha ba.
A dai shafinsa na Twitter Shugaban na Amurka ya wallafa cewa, ya yi ganawar da Xi na kasar China, inda ya ce tawagogin bangarorin biyu, za su yi wata ganawa ta sharar fage gabanin haduwar shugabannin biyu.
A ‘yan makonnin da suka gabata, zaman tattaunawa kan takaddamar cinikayya da kasashen biyu ke yi ta samu cikas, inda hukumomin Washington suka zargi China da janye jiki daga wata matsaya da suka cimma a tsakaninsu, zargin da Chinan ta musanta.