Tattaunawa da ake yi kan sabon tallafin ya kawo karshe yayin da Fadar White House da Majalisar dokokin Amurka suka gaza cimma matsaya kan yawan kudaden da ake bukata da kuma yadda za a tunkari agazawa jama’ar kasar da makarantu da kuma tsarin da za a bi wajen dakile yaduwar cutar ta COVID-19.
Babban wakilin shugaba Donald Trump a wannan zaman tattaunawa, Steven Mnuchin da ya kasance shi ne Sakataren Baitul Malin Amurka , ya yi yunkurin farfado da tattaunawar.
Amma shugabar Majalisar wakilai, Nancy Pelosi da shugaban ‘yan Democrat a majaklisar dattawa Chuck Schumer sun yi fatali da bukatarsa wacce suka ce “ba ta taka kara ta karya ba,” suna masu cewa gwamnatin Trump sun cije a wuri daya.
Shugaba Trump dai ya dora laifin rashin samar da karin tallafi akan ‘yan Democrat wadanda ya ce “sun rike wuyan Amurkawa.”