Shugaban Amurka Donald Trump yace yana sa ran ganin an gudanar da ganawarsa da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, a cikin watan Mayu ko kuma farkon watan Yuni.
Kalaman nasa na jiya Litinin sun biyo bayan kalaman jami’an Amurka dake tabbatar da cewa Kim ya amince ya tattauna batun wargaza makaman nukliya a yankin na Koriya.
Wannan ita ce babbar alamar dake tabbatar da shugaba Kim har yanzu a shirye yake ya gana da shugaba Trump tun lokacin da ita Koriya din ta bada shawarar taron koli a watan da ya gabata.
Sai dai babu wani karin bayani a kan abubuwan da za a tattauna akai da kuma inda za a yi tattaunawar.
Amma kuma jami’an Amurka sun ce kasashen biyu suna tuntubar juna cikin sirri.
Trump ya dade yana nanata kiran da a wargaza duk wani shirin Nukiliya a makurdin na Koriya.