Trump Na Barazanar Rufe Harkokin Gwamnati

Donald Trump

Shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi barazanar dakatar da dukkan al'amuran gwamnati idan majalisa bata amince da gina katanga akan iyakar Amurka da Mexico ba domin dakile shigowar bakin haure ba.

Shugaban na Amurka yayi ikirarin cewa yan jami'iyyar Demokrat dole su bashi goyon baya kan tsaron iyaka wanda ciki har da ginin katanga, da wadansu tsauraran canje canje kan harkokin shige da ficen kasar, amma saboda majalisar na da karancin ‘yan jam'iyyar shi Trump din ta Republican wacce kuma yawancin su ‘yan Democrat ne, sun ki kuma amincewa da kudurin trump din na yin sauyi kan harkokin shige da fice sau biyu a makonnin bayan nan.


Barazanar tsayar da harkokin gwamnatin da Trump yayi na zuwa ne a daidai lokacin da izinin kashe kudi yake gab da karewa a karshen watan satumba , hakan kuma na zuwa ne makonni biyar kafin zaben 'yan majalisar dattijai. Yawanci ‘yan majalisar dokokin Amurka na cimma matsaya kan kashe kudi kafin kudin su kare kamar yadda ya faru a shekarar da ta gabata.

‘Yan majalisar jam'iyyar democrat da dama, sunyi amfani da shafukan su na twitter wajen sukar barazanar da trump yake na rufe harkokin gwamnati.