Trump Zai Zanta Da Shugaba Xi Jinping Na China Kan Rikici Da Koriya Ta Arewa.

Shugaba Donald Trump na Amurka

Shugaba Trump yace idan har Koriya Ta Arewa ta kuskura ta kawo wa Amurka hari zata dandana kudarta.

Shugaban Amurka Donald Trump, yace zai yi magana ta woyar tarho da shugaban Sin ko China Xi Jinping, a daren jiya jumma'a, kan abunda ya kira "mummunar yanayi" da Koriya Ta Arewa

Haka nan ya sake nanata gargadi da yayi kan Koriya Ta Arewa, kan irin barazana da take-takenta kan Amurka, yana cewa "idan wani abu ya faru da Guam, koriya ta Arewa zata fuskanci mummunar damuwa." Hukumomin kasar dake Pyongyang, sun yi barazanar aikewa da makamai masu linzami zuwa yankin dake karkashin Amurka a yankin tekun pacific, wadda ya kasance babbar tungar mayakan Amurka.

Da yake magana da manema labarai tun farko a jiya jumma'a, a gidansa mai filin wasan kwallon Golf dake jahar New Jersey,Trump yace Amurka tana tunanin daukar karin wasu matakan azawa KTA takunkumin karya tattalin arziki "masu tsanani."