Zaman doya da manja tsakanin Fadar Shugaban Amurka da bangaren jami’an tsaron farin kaya na karuwa, yayin da Shugaba Donald Trump da tsohon babban shugaban jami’an tsaron farin kaya ke ta kace-nace kan takardar tabbatar zama masanin tsaro.
Jiya Jumma’a Shugaba Trump ya kai bugunsa na farko a wannan dauki ba dadin da ake yi, ya na mai barazanar janye takardar tabbatar zama masanin tsaro ta wani babban jami’in Ma’aikatar Shari’a, sannan ya kare shawarar da ya yanke ta soke takardar tabbatar da zama masanin tsaro ta tsohon shugaban hukumar leken asirin tsaron kasa ta CIA John Brennan tare da cewa mutane da dama sun yaba da hakan.
Daga bisani, tsofin jami’an hukumar CIA sun mai da martani, inda fiye da 60 daga cikinsu su ka rattaba hannu kan wata takarda ta yi Allah wadai da abin da su ka kira, “ramuwar gayyar siyasa kan jami’an tsaron farin kaya da sauran kwararru kan harkar tsaro.”