Kakakin fadar shugaban Amurka mai jiran gado Sean Spicer, yana gayawa Amurkawa kada su yi zumudin tsammanin shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump zai bayyana wani sabon bayani dangane da sakamkon binciken da hukumomin leken asirin Amurka suka gudanar dangane da kutse a komputocin abokan hamayyar siyasar Donald Trump da suka fallasa, wanda ake ganin ya taimakawa Trump din ya lashe zabe.
WASHINGTON DC —
Spicer, ya gayawa tashar talabijin ta CNN jiya Litinin cewa,yana shugaban mai jiran gado bayan ganawarsa da shugabannin hukumomin leken asiri irin hukuncinda ya yanke kan rahoton da suka gabatar,da kuma shi irin fahimtarsa, kuma ya tabbatar da cewa jama'a sun fahimci cewa akwai ayoyin tambaya kan wannan batu.
Trump ya gayawa manema labarai a jajiberen sabuwar shekara cewa, yana da bayanai fiyeda abunda jama'a suka sani dangane da zargin Moscow tayi katsalandan a zaben Amurka.
Shugaban na Amurka mai jiran gado ya bayyana shakku kan sakamakon binciken da hukumomin leken asiri suka yi wanda yace Rasha tayi kutsen.