Trump Ba Ya Son Mueller Ya Bayyana Gaban Majalisa

Shugaba Donald Trump ya fada a jiya Lahadi cewa kada mai bincike na musamman Robert Muller ya bayyana gaban majalisar ya bada bahasi, lamarin da ya sabawa matsayar shugaban ta baya cewa ya bar wannan sahawarar ga Antoni janar.

Ya yin da tankiya ke kara tsanani, inda ‘yan Democrats a majalisar wakilai suke kokarin kawo Muller gaban kwamitin shari’ar majalisar, Trump ya fada a wani sakon Twitter babu wata dama da ta ragewa ‘yan Democrats, Ya kuma kara da cewa, Shin suna so su sake duban ne, saboda suna jin haushin an gano babu wani hadin baki.

‘Yan Democrats suna neman karin bayani a kan rahoton da Muller ya fitar a kan binciken Rasha. Shugaban kwamitin shari’a a majalisar dattawa Lindsey Graham yace ba shi da niyar gayyatar Muller ya bada bahasi a kan rahotonsa ba.

Trump ya fadawa manema labarai a ofishinsa na Oval a makon da ya gabata cewa bada bahasi da Muller zai yi ya ta’allaka ne a kan Antoni janar. Shiko William Barr yace bashi da matsala da bahasi da Muller zai bayar.