Tottenham Hotspur Ta Kori Jose Mourinho

Jose Mourinho

Sallamar ta Mourinho na zuwa ne bayan da ya kwashe wata 17 yana horar da 'yan wasan na Hotspur.

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur, ta kori Jose Mourinho daga matsayinsa na mai horar da ‘yan wasan kungiyar ta Ingila.

Tottenham ta bayyana hakan ne a yau Litinin a shafinta na Twitter, inda ta fadada bayaninta da cewa, ta sallami daukacin tawagar masu horar da ‘yan wasan kungiyar wacce Mourinho ke jagoranta.

"A yau, kungiyar na mai sanar da cewa, mun sallami Jose Mourinho da sauran tawagar masu horar da 'yan wasan, wadanda suka hada da, Joao Sacramento, Nuno Santos, Carlos Lalin da Giovanni Cerra." Kungiyar ta fada a shafinta na @SpursOfficial.

Sallamar ta Mourinho na zuwa ne bayan da ya kwashe wata 17 yana horar da 'yan wasan na Hotspur.

Dan shekara 58, Mourinho ya sha kaye a wasa 13 a gasa daban-daban da ake bugawa a kasar ta Ingila a wannan kakar wasa.

Wannan shi ne kaye mafi yawa da ya taba sha a tarihin aikinsa na horar da ‘yan wasa, kuma akwai rahotanni da suka nuna cewa ‘yan wasansa sun gaji da wata sara da ya dauko, ta yi musu fada a baina jama’a a duk lokacin da suka sha kaye.

A watan Nuwambar shekarar 2019, Mourinho ya karbi ragamar tafiyar da kungiyar daga hannun Mauricio Pochettino.

Waye Zai Maye Gurbin Mourinho?

Your browser doesn’t support HTML5

Waye Zai Maye Gurbin Jose Mourinho?

Kocin RB Leipzig Julian Nagelmann shi ne a gaba-gaba cikin wadanda ake tunanin za su maye gurbin Jose Mourinho a kungiyar Tottenham Hotspur – a cewar marubatan kasar Ingila.

Ko da yake, ana kuma alakanta kocin na Jamus da zuwa kungiyar Bayern Munich.

Mutum na biyu shi ne, kocin Leicester City na yanzu, wato Brendan Rodgers.