Tinubu Zai Halarci Taron Kolin Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka Ta AU A Addis Ababa

Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu zai bar Abuja a gobe Alhamis zuwa birnin Addis Ababa na kasar Habasha domin halartar babban taron shugabannin kungiyar AU ta tarayyar kasashen Afirka.

Babban Hadimin Shugaba Tinubu akan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar daya fitar a yau Laraba

Yace Tinubu zai hadu da sauran shugabannin kasashen Afirka a wani taron kolin da zai gudana akan yin garanbawul ga kungiyar ta AU da batun zaman lafiya da tsaro da kuma muhimman batutuwa irinsu sauyin yanayi da tsare-tsaren yadda za’a rika gudanar da taro da al’amuran da za’a baiwa fififko yayin taron kungiyar G20; ta kasashen ashirin mafi karfin arziki a duniya.

A cewar mai magana da yawun Shugaban Kasar, taken taron kolin kungiyar AU na bana shine: “baiwa dan Afirka ilmin daya dace da karni na ashirin da daya. Samar da nagartaccen tsarin ilmin da zai samar da karin damammaki na yin tafiya tare domin samun ingantaccen ilmin daya dace da al’ummar Afirka tsawon rayuwa.”

Haka kuma, Shugaba Tinubu zai halarci taron kolin kungiyar ECOWAS, ta bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma a matsayinsa na Shugabanta.

Ministoci da manyan jami’an gwamnatin Najeriya ne zasu yiwa Shugaban rakiya yayin wannan tafiya.

Ana sa ran Shugaban ya dawo fadarsa dake Abuja bayan kammala tarurrukan.