Tinubu Ya Taya Joseph Boakai Murnar Lashe Zaben Laberiya 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)

Shugaba Tinubu ya kuma jinjinawa Shugaba George Weah da ya amince da shan kaye, matakin da ya ce zai taimaka wajen kaucewa ta da hargitsin siyasa. 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya Joseph Boakai murnar samun nasara a zaben shugaban kasa da aka yi a Laberiya.

Cikin wata sanarwa da kakakin Tinubu, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Asabar, shugaban na Najeriya ya kuma taya al’umar kasar ta Laberiya murnar gudanar da zaben cikin lumana.

Shugaba Tinubu ya kuma jinjinawa Shugaba George Weah da ya amince da shan kaye, matakin da ya ce zai kaucewa ta da hargitsin siyasa.

“Wannan babban abin misali da Weah ya nuna “a tsarin dimokradiyya, abin a yaba ne musamman a wannan lokaci da muke ciki a yankin Yammacin Afirka yayin da tsarin dimokradiyya ke fuskantar barazanar masu kokarin haifar da cikas.” Tinubu ya ce a sanarwar.

Jami’an zabe sun ce cikin kuri’u kashi 99.598 da aka kidaya a zaben da aka yi a ranar Talata, Boakai ya samu kashi 50.89 cikin 100 yayin da Weah ya samu kashi 49.11 cikin 100 na kuri’un da aka kada.

Wannan sakamakon zabe ya yi daidai da wanda aka yi shekaru shida da suka gabata a lokacin da Weah ya kada Boakai a zagaye na biyu.