WASHINGTON, D.C.- A ranar Litinin ne shugaba Bola Tinubu ya tashi domin halartar taron kasashen na G20 da za a yi a kasar Indiya bisa gayyatar da Firai Minista Narendra Modi ya yi masa, in ji kakakinsa Ajuri Ngelale.
A yanzu dai Afirka ta Kudu ita ce mambar Afirka daya tilo a cikin rukunin kasashe 20 masu karfin masana'antu a duniya.
“Yayin da kasancewar Najeriya a cikin kungiyar G-20 yana da kyau, gwamnati ta fara tuntubar juna da nufin tabbatar da alfanu da kasadar zama memba,” in ji Ngelale a cikin wata sanarwa.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne, Ngelale ya ce Tinubu zai halarci taron G20 ne domin kokarin inganta zuba jari a Najeriya da kuma tattaro jarin duniya zuwa cikin kasar don bunkasa ababen more rayuwa.
Sabuwar gwamnatin Najeriya na son karfafa saka hannun jari maimakon dogaro da cin bashi don samar da ayyukan yi yayin da take kokarin farfado da tattalin arzikin da ke fama da basussuka, da karancin kudi, hauhawar farashi mai da kuma samar da wutar lantarki.
Tinubu dai ya fara daukan wasu muhimman matakai da Najeriyar ba ta taba gani ba cikin gomman shekaru.
Sai dai sun jefa al’umar kasar cikin yanayi na tsadar rayuwa.
-Reuters