Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tafi Faransa a sabon jirgin Airbus A330 da aka saya masa a cewar fadar shugaban kasa.
Jirgin ya maye gurbin tsohon da shugabannin Najeriya suka kwashe shekaru 19 ana amfani da shi in ji Kakakin Tinubu Bayo Onanuga.
“Wannan sabon jirgi da aka sayo a farashi mai rahusa, ya sa Najeriya za ta kauce wa kashe miliyoyin daloli wajen gyara da sayen mai a kowace shekara.” Onanuga ya ce a wani sako da ya wallafa a shafin Twitter a ranar Litinin.
Tun a zamanin tsohoNn Shugaba Olusegun Obasanjo ake amfani da tsohon jirgin a cewar shi.
Maye gurbin tsohon jirgin mai lamba B737 – 700 (BBJ) ya biyo bayan zaman jin bahasi da majalisar dokokin Najeriya ta yi kan lafiyar jirgin da kuma kudin gyaransa, “musamman bayan da ya lalace yayin wata tafiya da aka yi da shi zuwa Saudiyya.”
Kwamitin kula da sha’anin tsaro da bayanan sirri na Majalisar Dattawa ne ya ba da shawara a sauya jirgin wanda “ya riga ya tusfa domin a rage kudaden da ake kashe masa.”
Sai dai fadar shugaban Najeriyar ba ta fadi a nawa aka sayi jirgin ba.