Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da yin wani gagarumin garanbawul a jami’o’in gwamnatin tarayyar kasar da dama, ciki har da Jami’ar Abuja, da yanzu aka sauya wa suna zuwa Jami’ar Yakubu Gowon.
Da take tabbatar da sauye-sauyen, sanarwar da mashawarcin shugaban Najeriyar na musamman a kan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, yace sauye-sauyen sun fara aiki ne nan take.
Shugaba Tinubu ya rushe majalisar gudanarwar jami’ar tare da sauke Farfesa Aisha Sani Maikudi daga kan mukaminta na shugabancin Jami’ar Yakubu Gowon.
An kuma nada shugaban majalisar gudanarwar jami’ar aikin gona ta Makurdi na yanzu, Sanata Lanretejuoso a matsayin shugaban majalisar gudanarwar jami’ar ta Yakubu Gowon.
Sanata Joy Emordi wanda ke zama shugabar majalisar gudanarwar jami’ar Alvan Ikoku za ta maye gurbinsa a jami’ar aikin gona ta Makurdi.
Shugaba Tinubu ya kuma nada Farfesa Lar Patricia Manko a matsayin shugabar Jami’ar Yakubu Gowon ta riko tsawon wa’adin watanni 6.
Ba za ta cancanci shiga takarar zama cikakkiyar shugabar jami’ar ba idan wa'adin ta ya kare.
Ku Duba Wannan Ma Wasu Malamai Sun Yi Zargin Rashin Bin Ka'ida Wajen Nada Shugabar Jami'ar Abuja... Ku Duba Wannan Ma Gwamnatin Najeriya Ta Sauya Sunan Jami' ar Abuja Zuwa Ta Yakubu Gowon