Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Malamai Sun Yi Zargin Rashin Bin Ka'ida Wajen Nada Shugabar Jami'ar Abuja...


Prof. Aisha Sani Maikudi - Newly Appointed Vice-Chancellor University of Abuja
Prof. Aisha Sani Maikudi - Newly Appointed Vice-Chancellor University of Abuja

Malaman sun yi zargi sabuwar Majalisar Gudanarwar Jami'ar da kaucewa bin tsari wajen nada Farfesa Aisha Sani Maikudi a matsayin shugabar Jami'ar, said ai kuma awkai amma kuma akwai wani rukunin Malaman da suka ce zargin ba shi da tushe.

Rahotanni sun nuna cewa rikici mai tsanani ya kunno kai akan tsarin nada sabuwar Shugabar Jami'ar Abuja da aka yi a makon da ya gabata. Lamarin da ya sa wasu Malaman Jami'ar sama da 50 suka nufi kotu don kai kukan su.

Malaman sun yi zargi sabuwar Majalisar Gudanarwar Jami'ar da kaucewa bin tsari wajen nada Farfesa Aisha Sani Maikudi a matsayin shugabar Jami'ar, said ai kuma awkai amma kuma akwai wani rukunin Malaman da suka ce zargin ba shi da tushe.

Matakin farko da ake dauka idan aka samu gurbi a shugabancin Jami'a, shine a tallata matsayin Shugaban Jami'ar, sannan, sai a tantance sharudan cancanta da ake bukata duk wanda yake sa sha'awar shugabancin jami'ar ya cika.

Wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda ta ruwaito cewa, sabanin haka, wasu masu neman cike gurbin shugaban jami’ar sun ce ba a tallata girbin ba kamar yadda doka ta tanadar, wasu kuma sun ce an tallata amma kuma an sanya tsauraran ka’idoji.

Farfesa Rosemary Udeozo tana cikin rukunin malaman jami'ar dake kalubalantar tsarin da aka yi aiki da shi. Farfesa Rosemary ta ce wannan shi ne karon farko da za a nada Shugaba a Jami'ar ba tare da wakilai daga bangaren gwamnati da za su sa ido akan tsarin zaben shugaban balle kuma wakilan kwamitin gudanarwa ta Jami'ar.

Madina ta ruwaito cewa, wani Malamin Jami'ar wanda ya dade yana aiki a wurin, Farfesa Abubakar Umar Kari ya mai da martani kan wannan zargi yana mai cewa akwai rashin fahimta da farfaganda a cikin al'amarin, wanda ya kai ga wasu tsiraru suke neman ta da hayaniya.

A saurari rahoton Medina Dauda:

UNIABUJA VS VC CRISIS -----REPORT.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG